fbpx
lang

KUNGIYOTIN TAADDANCI DA HADARORINSU GA AL,UMMA

Ta,adanci da akaye dasunan addini shine babban chuta da take lalata al,umma, kuma take chire son juna tsakanin mutane, kuna tana gusar da hankulan al,umma, takuma cere musu kauna da son juna , daga karshe sai al,umma talalace gaba daya, duk dacewa su har kullum cewa suke sune suke kawo chigaba a al,umma wadda aikinsu yanuna kishiyan abunda suke fada, yadda suke lalata tarihin al,umma kuma suke raba uwa da danta kai harma su sace yan,mata suje suna lalata dasu dasunan jihadi, saboda haka wanan mutane duk inda sukaje lalata wajan sukeyi , misali kamar yan da,ish a kasar Siriya da Iraki dakuma Libiya dakuma yan, boko haram a Nigeria dama wasunsu wanda bamu ambacesu ba.
GA KADAN DAGA CIKIN AIYUKANSU WANDA TARIHI YAGANI :
NAFARKO : LALATA TATTALIN ARZIKIN KASAR DA SUKA SHIGA DAMA MAKUBCIYARTA
Hakika bincike ya tabbbatar da cewa lalacewan tattalin arzikin kasar Siriya da kasashen da ke kewaye da ita wanda tattalin arzikinsu yayi kasa sosai tun daga 2011 zuwa yanzu sakamakon rashin shuguwan yan kasuwa damasu zuwa yawan bude ido, wanda hakan yafarune sakamakon tashin tashina da yan tada kayan bayan sukeyi da sunan musulunci, wanda hakan yasa talauci ya karu sosai masu kudi suka karye yan kasa suka rasa aikin yi , mata suka fara bara akan titian, wasu suka rasa inda zasu sa kansu, hakan ya farune sakamakon aiyukan ta,addanci da masu tada kayan baya sukayi da sunan musulunci
ABU NA BIYU : LALATA WAYEWA DA AL,ADUN KIRKI DASUKEYI A DUK KASAR DA SUKA SHIGA
Kamar yadda muka gani duk inda suka shiga suna kokarin suga andaina karatun zamani! wanda su suna ganin yin karatun zamani kafirce ne a wajansu!! saboda haka suke kokarin hanawa, wanda hakan yakan kawo tasgaro ga al,umma.
Sanann suna lalata wuraran tarihin al,umma kamar yadda suka lalata hulab a Siriya, suka lalata wurare masu yawa na addini dana tarihi a Kasar Iraki da Libiya da kuma Afganistan dama sauran kasashan dabamu ambacesu ba, wanda hakan dasukayi ya lalata cigaban kasashan , su kuma aganinsu hakan dasukayi jihadi ne , saboda a akidarsu wuraran tarihi gumakaine, sun manta da cewa alkura,ani mai girma yagaya mana muyi yawo abayan kasa muga ababan dasuka faru.
ABU NA UKU : TADA HANKALIN GARINDA SUKA SHIGA DA KUMA KONA MUSU MAHALINSU
Tabbas masu tada kayan baya dasunan addini sun kokkona gidaddajin al,umma kuma sun raba dayawa da iya yansu wasuma sun bar gidaddajinsu sakamakon ayukan masu tada kayan baya, wasu mata kuma sun maidasu bayi, suna abinda sukeso dasu har suna iya yimusu fade har suna iya haifuwa dasu ta wannan hanyar.

ABU NA HUDU : KASHE YARA DASUKEYI TA HANYAR YIN AMFANI DASU WAJAN YIN AIKIN TAADDANCI
Hakika kakan yabaiyana ga al,umma yadda suke amfani da yara kanana wajan yin ta,addanci yadda suke sa bam ajikin yaran suje su tayar sukashi kansu da sauran al,umma ko kuma ta wata hanyar daban bawannnaba
Ko shakka babu wannan tunane nasu na amfani da yara wajan yin aikin ta,addanci abune mai munin gaske, wanda zai lalata al,umman dazasu zo gobe wanda in hakan yaci gaba da kasan cewa to sufa zasu tasu ne cikin yaki da kashe-kashen mutane kamar yadda ake ganin aiyukansu nayau da kullum.
Ayukan masu tada kayan baya dasunan addini baitsaya ananba yakaiga suna iya yin abubuwanda karema bazaiyiba idan har zasu samu su cika burinsu na kasha al,umman da basa tare dasu,
Wannan kadanne daga cikin aiyukan da masu tada kayan baya sukeyi da sunan addini, na lalata kasashensu dama sauran kasashe

اظهر المزيد

مقالات ذات صلة

اترك تعليقاً

لن يتم نشر عنوان بريدك الإلكتروني. الحقول الإلزامية مشار إليها بـ *

شاهد أيضاً

إغلاق